logo

HAUSA

Sin ta cimma nasarar harba sabbin taurarin dan Adam guda 6

2022-07-27 15:12:11 CMG Hausa

Da misalin karfe 12 da minti 12 na safiyar yau Laraba, kasar Sin ta cimma nasarar harba roka mai dauke da taurarin dan Adam samfurin Lijian-1, daga cibiyar harba taurarin dan Adam ta Jiuquan. A wannan karo wannan roka, ta ratsa samaniya dauke da taurarin dan Adam guda 6 kamar yadda aka tsara.

Bisa labarin da aka samu, cibiyar kimiyya ta kasar Sin ce ta kera wannan roka, kuma za a yi amfani da wadannan taurarin dan Adam guda 6 da aka harba a fannonin binciken sararin samaniya, da kuma nazarin yanayin iska da sauransu. (Maryam)