logo

HAUSA

Babban bankin kasar Ghana ya tsayar da kudin ruwa kan kaso 19 bisa dari

2022-07-26 10:33:11 CMG Hausa

Babban bankin kasar Ghana ya tsayar da kudin ruwa kan kaso 19 bisa dari, da nufin dakile tasirin hauhawar farashin kayayyaki, da sauran abubuwa masu nasaba da raya tattalin arziki.

Gwamnan babban bankin kasar Ernest Addison ne ya sanar da hakan, yayin taron manema labarai, bayan zama na 107 na kwamitin tsara manufofin kudin kasar.

Da yake tsokaci kan hakan, Mr. Addison ya ce "Hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da kamari. Duk da cewa akwai tasirin sauyin yanayin shigar hajoji kasuwanni, a daya hannun kuma, sauyin farashin kayayyakin bukata na yau da kullum ya karu matuka."

Gwamnan bankin na Ghana ya kara da cewa, hauhawar farashin kayayyaki a watannin Afirili, da Mayu, da Yuni, ya yi tasiri ga farashin albarkatun man fetur, da kudaden sufuri, da karyewar darajar kudin kasar, da kuma tsadar kayan abinci.   (Saminu Alhassan)