logo

HAUSA

Guterres ya nada jami'in diplomasiyyar kasar Sin Li Junhua a matsayin mataimakinsa

2022-07-26 14:19:08 CMG Hausa

A jiya Litinin ne, babban sakataren MDD António Guterres ya sanar da nadin jami'in diplomasiyyar kasar Sin Li Junhua, a matsayin mataimakinsa mai kula da harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’umma.

Bisa sanarwar da offishin kakakin babban sakataren MDD ya bayar, an ce, Li Junhua zai maye gurbin Liu Zhenmin wanda shi ma jami’in diflomasiyya ne daga kasar Sin. Guterres ya godewa Liu Zhenmin, bisa rawar gani da ya taka yayin da yake aiki a matsayin mataimakin shugaban MDD.

Sanarwar ta ce, Li Junhua zai ba da ra’ayoyinsa, da burinsa a fannin inganta tattalin arzikin bangarori daban daban, da kuma hadin gwiwar zamantakewar al’umma, ya kuma yi alkawarin cewa, zai ci gaba da gudanar da ajandar ci gaba mai dorewa ta MDD, ta nan da shekarar 2030, ta yadda zai sadaukar da kai da bauta wa kasashen membobin MDD.

Kafin nadin nasa, Li ya taka rawar gani, a taruka masu yawa na kwamitin tattalin arzikin al’ummar kasashen yankin Asiya da Pasific na MDD, da kwamitin sulhu na MDD, da kuma sauran taruka na bangarori daban daban, kamar kungiyar G20, da kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasashen yankin Asiya da Pasific, da taron kasashen yankin Asiya da Turai, da kasashen BRICS da dai sauransu. (Safiyah Ma)