logo

HAUSA

Masanin Amurka: Tattalin arzikin Amurka na tabarbarewa cikin sauri

2022-07-26 10:58:39 CMG Hausa

Jiya Litinin, sheihun malamin ilmin tattalin arziki a kwalejin Saint Mary ta kasar Amurka Jack Rasmus, ya zanta da manema labarai, inda ya yi tsokaci da cewa, alkaluman da aka fitar a baya bayan nan sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Amurka yana tabarbarewa cikin sauri, kuma zai kara samun koma baya nan da watan Satumban bana.

Jack Rasmus ya kara da cewa, alkaluman da aka fitar sun tunatar da cewa, a halin yanzu, jarin da ake zubawa a kasar Amurka ya ragu, kuma kudin da ake kashewa bai karu ba, saboda tasirin raguwar darajar kudi, duk wadannan na nuna cewa, tattalin arzikin Amurka yana tabarbarewa cikin sauri. (Jamila)