logo

HAUSA

An bude taron dandalin kare hakkin dan Adam na Beijing na shekarar 2022

2022-07-26 20:17:43 CMG Hausa

A yau ne, aka bude taron dandalin tattaunawa kan kare hakkin dan Adam na Beijing na shekarar 2022, bisa taken “adalci, da amincewa da bambance-bambance don sa kaimi ga raya sha’anin kare hakkin dan Adam”. Kusan mutane 200 da suka hada da manyan jami’ai da masana da daga kasashe kimanin 70 da kungiyoyin kasa da kasa ciki har da MDD, da wakilan diflomasiya dake kasar Sin ne suka halarci taron.

Shugaban kungiyar nazarin kare hakkin dan Adam ta kasar Sin Baimachilin ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, tun bayan babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta Sin karo na 18, kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta Sin, ya ke dora muhimmanci kan mutunta da kare hakkin dan Adam a matsayin muhimmin aikin gwamnatin kasar. Jama’ar kasar Sin fiye da biliyan 1 da miliyan 400 sun kara jin dadin zaman rayuwa da tsaro da tabbatar da hakkinsu na dogon lokaci. A halin yanzu, duniya ta shiga wani sabon yanayi na tashin hankali da sauye-sauye, kuma an kawo cikas wajen aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa nan da shekarar 2030 da MDD ta tsara, kamata ya yi kasa da kasa su tsaya kan hanyar makoma ta bai daya, da hada kai da amincewa da bambance-bambance, da yin tattaunawa cikin adalci, da cimma daidaito da magance matsalolinsu, ta cimma yarjejeniyar bunkasa sha’anin kare hakkin dan Adam, don inganta jin dadin jama’a, da kuma kyautata harkokin kare hakkin dan Adam a duniya baki daya.

Shugaban majalisar wakilai ta kasar Liberia Bhofal Chambers, ya yaba da kokarin da jam’iyyar kwaminis ta Sin da gwamnatin kasar Sin suke yi, wajen daidaita matsalar hakkin dan Adam na duniya. Ya kuma yi iyamin cewa, kasar Sin tana da karfin inganta da kiyaye hakkin bil-adama a duniya. (Zainab)