logo

HAUSA

Tagwayen titunan mota na kasar Sin sun hade kaso 95 bisa dari na al’ummun kasar

2022-07-26 10:56:28 CMG Hausa

Kasar Sin ta kafa kakkarfan ginshiki a fannin gina manyan titunan mota, domin hade sassa daban daban na yankunan kasar, da saukaka zirga zirgar ababen hawa, kuma tuni wadannan manyan tituna suka hade kimanin kaso 95 bisa dira na yankunan kasar.

Da yake karin haske game da hakan, yayin wani taron manema labarai a jiya Litinin, jami’i a ma’aikatar sufuri ta kasar Wang Tai, ya ce a yanzu haka, manyan hanyoyin kasar sun hade kaso 98.8 bisa dari na birane masu yanwan al’ummar da suka zarta 200,000, da manyan yankunan gudanarwa, yayin da irin wadannan manyan tituna suka game kusan kaso 88 bisa dari, na sassan dake da matsayi na gunduma.

Wang ya kara da cewa, manyan hanyoyin mota dake kasar Sin sun hade dukkanin yankunan gudanarwan dake sama da matsayin gunduma, da daukacin masu iyaka da tashoshin ruwa da ake amfani da su a duk tsawon shekara.

Ya ce ya zuwa karshen shekarar da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta gina tagwayen hanyoyin mota da tsayinsu ya kai kilomita 117,000, inda kuma aka budewa matafiya manyan titunan mota da tsayinsu ya kai kilomita 257,700.

A farkon shekarar bana, mahukuntan kasar Sin sun fitar da wata takardar sanarwa, dake bayyana burin gina manyan hanyoyin mota na kasa nan da shekarar 2035, da za su kai tsayin kilomita kusan 461,000, wadanda za su kunshi tagwayen hanyoyi masu tsayin kilomita 162,000, da manyan tituna dake hade manyan sassa masu tsayin kilomita 299,000. (Saminu Alhassan)