logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Yi Maraba Da Kokarin Da Bangarorin Libya Ke Yi Na Tabbatar Da Hako Mai Yadda Ya Kamata

2022-07-26 19:56:45 CMG Hausa

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya yi maraba da kokarin da bangarorin kasar Libya ke yi, wajen tabbatar da hako mai a kasar yadda ya kamata.

Wakilin na kasar Sin ya shaidawa taron kwamitin sulhu na MDD game da kasar Libya cewa, kasarsa tana maraba da yadda bangarorin kasar Libya suke kokarin kawar da tsoma bakin siyasa, da yin shawarwari, da warware sabanin ra'ayi kan harkokin tafiyar da bangaren man fetur, da rarraba kudaden shiga, da kuma tabbatar da tsarin samar da mai a kasar Libya yadda ya kamata.

Dai Bing ya bayyana man Fetur a matsayin "muhimmin tushen samun kudin shiga don sake gina kasa da inganta rayuwar jama’a a Libya. Yana mai cewa, ya kamata a ci gaba da tafiyar da masana'antar mai ta Libya a karkashin kulawar kasar, kuma a yi amfani da dukkan kudaden shigar man fetur din don amfanin al'ummarta."

Ya kuma bayyana cewa, kadarorin kasar da aka kwace, wata muhimmiyar hanya ce ta sake gina kasa. Kuma ya kamata kasashen da abin ya shafa, su kula da kadarorin da aka kwace, kamar yadda kudirin kwamitin sulhu ya tanada.(Ibrahim)