logo

HAUSA

Xi Ya Tattauna Da Takwaransa Na Kasar Indonesia

2022-07-26 20:36:34 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da takwaransa na kasar Indonesia Joko Widodo da ke ziyara a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.

Xi ya yi nuni da cewa, a karkashin jagorancin hadin gwiwarmu, dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia ta bunkasa cikin 'yan shekarun nan, inda ta nuna juriya da kuzari.

Bangarorin biyu sun karfafa amincewa da juna bisa manyan tsare-tsare da zurfafa hadin gwiwar siyasa, da tattalin arziki, da al'adu da na harkokin teku.

Haka kuma, kasashen suna nuna irin nauyin da ke bisa wuyansu, tare da samun nasarori masu gamsarwa wajen kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin, da inganta nuna goyon baya da hadin gwiwa a duniya, da nuna kyakkyawan misali ga manyan kasashe masu tasowa, wajen neman karfi ta hanyar hadin kai da cin moriyar juna.

Shugaba Xi ya ce, ya kamata bangarorin biyu su zurfafa hadin gwiwa mai inganci game da shawarar “ziri daya da hanya daya” da samar da karin sakamako.

Xi ya yi nuni da cewa, sauye-sauyen da ake fuskanta a duniya, suna bulla ta hanyoyin da ba a taba ganin irinsu ba. Don haka, ya kamata kasashen Sin da Indonesia, su yi aiki tare don nuna nauyin da ke bisa wuyansu a matsayinsu na manyan kasashe masu tasowa, da aiwatar da ra'ayin bangarori daban-daban na zahiri, da kiyaye bude kofa ga kasashen waje, da ba da hikimomi na kasashen dake gabashin duniya, da ba da gudummawar karfin Asiya wajen tafiyar da harkokin kasa da kasa.

A nasa jawabin kuwa, Joko Widodo ya bayyana cewa, kasashen Indonesia da Sin, abokan hulda ne bisa manyan tsare-tsare, kuma sun tsara muhimmin buri na gina al'umma mai makoma ta bai daya. Hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu, ta cin moriyar juna da samun nasara tare ce, wanda ba wai kawai tana kawo alfanu ga al'ummomin kasashen biyu ba, har ma tana bayar da muhimmiyar gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a shiyyar da ma duniya baki daya.

Ya kara da cewa, kasar Indonesia tana son yin aiki tare da kasar Sin, don ci gaba da zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu, da ba da babbar gudummawa ga zaman lafiya a yankin da ci gaban duk duniya.(Ibrahim)