logo

HAUSA

Ma’aikatar tsaron Sin: Abubuwan dake cikin takardar bayanin Japan game da Sin ba su da tushe

2022-07-26 15:44:13 CMG Hausa

Gwamnatin kasar Japan, ta fitar da takardar bayaninta ta bana a ranar 22 ga watan nan, inda aka bayyana cewa, kasar Sin tana boye manufar tsaronta da aikin ginin karfin rundunar sojin ta, kuma tana yin kokarin canja yanayin da ake ciki a tekun gabas da kuma tekun kudu, kana an kara wasu abubuwa dake shafar batun yankin Taiwan a cikin takardar.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Wu Qian, ya yi tsokaci da cewa, abubuwan da aka fada a cikin takardar ba su da tushe, kuma tsoma baki ne cikin harkokin gidan kasar Sin, don haka kasar Sin tana bakin ciki da adawa da hakan, ta kuma bukaci Japan da ta gyara kuskuren ta. (Jamila)