logo

HAUSA

Ministan Harkokin Wajen Sin Ya Jaddada Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin Domin Ci Gaban Yankin

2022-07-25 19:43:36 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya bayyana cewa, zaman lafiya da kwanciyar hankali a tekun kudancin kasar Sin, wani muhimmin sharadi ne na ci gaban yankin.

Wang ya bayyana hakan ne Litinin din nan, yayin da yake jawabi a bikin bude taron karawa juna sani, game da tunawa da cika shekaru 20 da rattaba hannu kan yarjejeniyar sassan da za su gudanar harkokin da suka shafi tekun kudancin kasar Sin (DOC) ta kafar bidiyo.

Yarjejeniyar ta DOC, ita ce takardar siyasa ta farko da kasar Sin da kasashen kungiyar ASEAN suka rattaba hannu a kanta, dangane da batun tekun kudancin kasar Sin.

Yana mai nuni da cewa, yarjejeniyar ta kuma tanadi muhimman ka'idoji na bai daya ga dukkan bangarorin kan daidaita batun tekun kudancin kasar Sin.

Ya kuma jaddada cewa, kasashen yankin su ne bangarorin da ke da alhakin daidaita batun tekun kudancin kasar Sin yadda ya kamata, Don haka, ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa, da su ci gaba da kiyaye tushen zaman lafiya a yankin.

Wang Yi ya ce, kamata ya yi dukkan bangarorin su goyi bayan duk wani mataki, da zai taimaka wajen sasantawa da magance rikice-rikice cikin lumana, da adawa da duk wasu kalamai da ayyukan da ke iya haifar da tashin hankali da ta da zaune tsaye a yankin.(Ibrahim)