logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Rasha na ziyara a Afrika, karon farko bayan barkewar rikicin kasar da Ukraine

2022-07-25 11:05:11 CMG Hausa

Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi ya gana da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov a birnin Cairo, inda suka tattauna game da dangantakar kasashen biyu da kuma batutuwan shiyya-shiyya da ma na duniya dake jan hankalinsu.

Sergei Lavrov ya mikawa shugaba Sisi wasikar da shugaban Rasha Vladimir Putin, wadda ta bayyana muhimmancin da Rasha ke ba dangantakarta da Masar, karkashin muhimmiyar yarjejeniyar hadin gwiwa dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, shugaban na Masar ya jinjinawa hadin gwiwar dake ci gaba da habaka tsakanin Masar da Rasha, bisa la’akari da ayyukan da Rasha ke yi a Masar din, kamar tashar makamashin nukiliya ta El-Dabaa da ake aikin gininsa yanzu haka da yankin raya masana’antu da Rasha ta kafa a yankin mashingin Suez da sauran wasu ayyukan hadin gwiwa a bangarori da dama.

Dangane da rikicin Rasha da Ukraine kuwa, Masar ta yi kira da a yi sulhu a siyasance.

Wannan shi ne rangadi na farko da Sergei Lavrov ke yi a nahiyar Afrika, tun bayan barkewar rikicin Rasha da Ukraine a watan Fabrerun bana. Rangadin zai kuma kunshi kasashen Habasha da Uganda da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo. (Fa’iza Mustapha)