logo

HAUSA

An kaddamar da dandalin tattaunawa kan al’adu karo na farko a Beijing

2022-07-25 14:52:21 CMG Hausa

An kaddamar da dandalin tattaunawa kan harkokin al’adu karo na farko a yau Litinin a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaban sashin fadakar da al’umma na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Huang Kunming ya halarci taron tare da gabatar da jawabin dake jaddada cewa, ya dace a raya dandalin al’adu na Beijing don ya zamanto wani dandali mai nagarta a fannin ba da shawarwari ga raya al’adu, da taimakawa ga kirkire-kirkiren al’adu, da kuma sa kaimi ga gina cibiyoyin al’adun kasar Sin, a wani kokari na bayar da sabuwar gudummawa ga gina kasar Sin mai karfin al’adu irin na tsarin gurguzu. (Murtala Zhang)