logo

HAUSA

Shugaban Iran: Dole ne a tabbatar da moriyar tattalin arzikin Iran idan ana son farfado da yarjejeniyar nukiliya ta kasar

2022-07-25 14:14:33 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na Xinhua ya labarta cewa, shugaban kasar Iran Seyed Ebrahim Raisi, ya ce ba za a cimma matsaya daya kan farfado da tattaunawa da yarjejeniyar nukiliya ta kasar ba, sai an warware batun kiyaye makaman nukiliya da tabbatar da za a ci gaba da bin yarjejeniyar da kuma tabbatar da moriyar tattalin arzikin Iran.

Bisa labarin shafin yanar gizo na shugaban kasar Iran, Raisi ya bayyana haka ne yayin da ya buga waya ga shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. A cewar Raisi, takunkumin da kasar Amurka ta kakaba wa kasar Iran ya haddasa mummunan tasiri ga tattalin arzikin fadin duniya, musamman nahiyar Turai. Ban da haka, ya nuna cewa, kudurin zargi kan rashin hadin gwiwa tsakanin kasar Iran da kungiyar IAEA da kungiyar IAEA ta zartar a ranar 8 ga watan Yuni ba shi da dalili.Safiyah Ma