logo

HAUSA

Ya kamata bangaren soja na Amurka ya dakatar da neman dalili kan fadada aikin soja a duniya

2022-07-25 20:42:53 CMG Hausa

A kwanakin baya, shugaban hafsan hafsoshin sojan kasar Amurka Mark Milley ya bayyana cewa, sojojin kasar Sin sun kara kaimi a cikin shekaru 5 da suka gabata. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana a yau cewa, kalaman kasar Amurka kan batun ba shi da tushe. Yawan kudin da Amurka take kashewa a fannin harkar soja shi ne a kan gaba a duniya, kana a kwanakin baya ta gabatar da daftarin kasafin kudin tsaro na kusan dalar Amurka biliyan 813 na sabuwar shekarar kasafin kudi. Kasar Amurka tana da sansanonin soja fiye da 800 a kasashen waje, kuma ba ta yi yaki ba tsawon shekaru 16 kawai tun bayan kafuwarta. Wasu jami’an kasar Amurka suna bin ra’ayoyin yakin cacar baka tsakanin kasashe masu tsarin jari-hujja da masu bin tsarin gurguzu da kuma yin takara a tsakanin kasa da kasa wadanda yawan ribar da suka samu ta yi daidai da yawan hasarar da sauran kasashe suka tabka, sun kuma bayyana wai barazanar kasar Sin don neman dalili na neman fadada sojojinsu. (Zainab)