logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Sakon Taya Murna Ga Taron Dandalin Tattaunawar Zaman Lafiya Da Tsaro Na Sin Da Afirka Karo Na Biyu

2022-07-25 20:54:36 CMG Hausa

Yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da wasikar taya murna ga taron dandalin tattaunawa kan zaman lafiya da tsaro na kasar Sin karo na biyu.

Xi ya jaddada cewa, kasashen Sin da Afirka abokai ne na kwarai, kuma abokan hulda, kana 'yan uwa na kwarai, wadanda ke tsayawa tsayin daka a kowane irin hali suna kuma taimakon juna.

A halin yanzu, duniya tana fuskantar manyan sauye-sauyen da ba a taba gani ba a cikin karni cikin sauri. Kuma har yanzu annobar COVID-19 tana yaduwa, kuma kalubalen tsaro daban-daban na ci gaba da bayyana, inda suke haifar da kalubalen da ba a taba ganin irinsa ba ga daukacin dan Adam.

Xi ya ce, tabbatar da zaman lafiya da tsaro mai dorewa a duniya, shi ne burin jama'ar Sin da Afirka na bai daya. Har kullum kasar Sin tana kiyaye tsarin hadin gwiwa da fahimtar juna na zahiri, da son yin hadin gwiwa tare da kawayen Afirka, da dagewa kan hada kai, da hadin gwiwa, da tabbatar da tsaro mai dorewa, da kiyaye MDD a matsayin tushen tsarin kasa da kasa, da kiyaye adalci a duniya, da yayata aiwatar da shirin tsaro na duniya, da gina kyakkyawar makomar al'ummar Sin da Afirka na sabon zamani.

An gudanar da taron dandalin tattaunawar zaman lafiya da tsaro na kasar Sin da Afirka karo na biyu, ta kafar bidiyo, bisa taken "Karfafa hadin gwiwa don samar da tsaro cikin hadin gwiwa". (Ibrahim)