logo

HAUSA

An hada na’urar Wentian da na’urar Tianhe a sararin samaniya

2022-07-25 10:58:54 CMG Hausa

Rahotanni daga ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) sun ce, bayan da aka yi nasarar harba na’urar Wentian, wani muhimmin bangare na farko na tashar binciken sararin samaniya, har ta shiga falaki cikin nasara, da misalin karfe 3 da minti 13 na safiyar yau Litinin 25 ga wata ne, na’urar Wentian ta yi nasarar hadewa da bangaren gaba na na’urar Tianhe a sararin samaniya, al’amarin da ya shafe tsawon awa 13.

Wannan shi ne karon farko da wasu manyan na’urorin binciken sararin samaniyar kasar Sin guda biyu, masu nauyin ton 20, wato Wentian da Tianhe, suka hade da juna a cikin falaki, kana karon farko da aka yi nasarar hada su, a yayin da ‘yan saman-jannati suke gudanar da ayyuka a cikin kumbo.

Har wa yau, sabbin rahotanni daga ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) sun ce, da misalin karfe 10 da minti 3 na safiyar yau Litinin 25 ga wata, ‘yan saman-jannatin kasar Sin wadanda suke aiki a cikin kumbon Shenzhou-14, sun yi nasarar shiga cikin na’urar Wentian. (Murtala Zhang)