logo

HAUSA

An yi taron karawa juna sani kan tunanin Xi Jinping game da harkokin diflomasiyya

2022-07-25 11:16:30 CMG Hausa

An yi taron karawa juna sani kan tunanin shugaba Xi Jinping dangane da harkokin diflomasiyya, jiya Lahadi a birnin Beijing, inda memban majalisar gudanarwar kasar, kana ministan harkokin waje, Wang Yi, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi.

Wang Yi ya jaddada cewa, ya dace a yi kokarin bude sabon babi ga harkokin diflomasiyyar kasar Sin mai salon musamman a cikin sabon zamanin da ake ciki, bisa jagorancin tunanin shugaba Xi kan tsarin gurguzu mai salon musamman na kasar a sabon zamani da tunaninsa kan harkokin diflomasiyya.

Wang ya kara da cewa, a matsayinsa na babban mai tsara fasalin harkokin diflomasiyya mai salon musamman na kasar Sin, Xi Jinping ya bullo da wasu jerin muhimman shawarwari da manufofi, inda ya kirkiro tunaninsa kan harkokin jakadanci, abun da ya zama tamkar alkibla ga harkokin diflomasiyyar kasar Sin, da samar da hikimomi da dabarun kasar wajen daidaita manyan batutuwan kasa da kasa, tare kuma da taimakawa ga ci gaban harkokin dan Adam.

A karkashin shugabancin tunanin Xi a fannin harkokin diflomasiyya, an ci gaba da gudanar da harkokin jakadanci masu salon musamman na kasar Sin daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kirkiro wani kyakkyawan muhalli ga cimma muradun kasar na farfado da al’ummar kasar baki daya, da bayar da babbar gudummawa ga sha’anin shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba ga daukacin bil’adama. (Murtala Zhang)