logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya Droupadi Murmu murnar zama sabuwar shugabar kasar Indiya

2022-07-25 16:36:41 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sako ga madam Droupadi Murmu a yau Litinin, inda ya taya ta murnar zama sabuwar shugabar kasar Indiya.

Xi ya ce, Sin da Indiya makwabtan juna ne, kana, kyakkyawar dangantakarsu na dacewa da muradunsu gami da na al’ummarsu baki daya, al’amarin da zai taimaka sosai wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da samar da ci gaba a wannan shiyya da ma duniya baki daya.

Xi ya kara da cewa, yana matukar maida hankali kan raya alakar kasarsa da kasar Indiya, kuma yana fatan yin kokari tare da shugaba Droupadi Murmu, don kara samun fahimtar juna a fannin siyasa, da zurfafa hadin-gwiwa, da shawo kan sabanin ra’ayi yadda ya kamata, ta yadda za’a ciyar da dangantakar kasashen biyu gaba bisa hanya madaidaiciya. (Murtala Zhang)