logo

HAUSA

AU ta yaba da yarjejeniyar fitar da hatsi da aka cimma tsakanin Rasha da Ukraine

2022-07-24 16:22:33 CMG Hausa

 

            

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya yaba da yarjejeniyar fitar da hatsin da kasashen Rasha da Ukraine suka rattaba hannu a kai a birnin Istanbul a ranar Juma'a tare da Türkiye da MDD.

Ministan tsaron Rasha Sergei Shoigu tare da takwaransa na Türkiye Hulusi Akar da babban sakataren MDD Antonio Guterres ne, suka fara sanya hannu kan yarjejeniyar wadda a hukumance ake kira "Initiative The Black Sea Grain Initiative", daga bisani kuma, ministan samar da ababen more rayuwa na Ukraine Oleksandr Kubrakov tare da sauran bangarorin biyu suka rattaba hannu.

Shugaban hukumar ta AU ya kuma taya shugaban kasar Senegal Macky Sall, kana shugaban karba-karba na kungiyar na yanzu, murnar sake dawo da hatsin da aka samarwa daga kasashen Rasha da Ukraine zuwa kasuwannin duniya.

Moussa Faki Mahamat ya yi imanin cewa, ziyarar da Sall ya kai Rasha da Ukraine a watan da ya gabata, ta taka rawa a wannan yarjejeniya.

Kasashen Rasha da Ukraine, su ne ke kan gaba wajen samar da burodi a duniya, inda suke samar da kusan kashi 1 bisa 3 na alkama da sha'ir a duniya, da kuma rabin man sunflower. Haka kuma, kasar Rasha, ita ce kan gaba wajen fitar da takin zamani a duniya da kuma albarkatun da ake samar da takin.(Ibrahim)