logo

HAUSA

Ana mai da hankali ga raya tattalin arziki ta fasahohin zamani a taron ci gaban matasan duniya

2022-07-24 17:05:56 CMG Hausa

Jiya ne, aka gudanar da taron dandalin tattaunawa kan tattalin arziki na fasahohin zamani na dandalin raya matasa na duniya a nan birnin Beijing, inda masana da wakilan matasa fiye da 20 daga sassan duniya suka halarci taron ta yanar gizo ko a wurin taron kai tsaye, don tattauna sabbin damammaki a fannin tattalin arziki ta fasahohin zamani.

A nata jawabin, wakiliyar hukumar shirin raya kasashe ta MDD Beate Trankmann ta bayyana cewa, sha’anin sadarwa ya kasance muhimmin bangare a rayuwar dan Adam da ba za a iya raba shi ba, kuma sabbin tunanin matasa, zai taimaka ga inganta sha’anin.

Mataimakin shugabar kungiyar harkokin matasa ta kasar Sin Fu Zhenbang ya yi bayyani da cewa, yana fatan matasa daga ko’ina a fadin duniya, za su tsara alkiblar ci gaba da ta dace, da amfani da damar da aka samu yayin ake yin kwaskwarima, da ci gaba da inganta kwarewarsu a fannin fasahar zamani da tunaninsu a fannin tattalin arzikin fasahohin zamani, da yin kokarin yin kirkire-kirkire a fannin raya tattalin arziki ta fasahohin zamani, don cimma burinsu na rayuwa.

Matasa daga kasashen Sin, da Indiya, da Bangladesh da sauransu sun yi bayanai da yin musayar ra’ayoyi da fasahohi a fannonin kiwon lafiya, da kiyaye muhalli da sauransu ta hanyar fasahohin zamani. (Zainab)