logo

HAUSA

Kasar Sin Harba Muhimmin Bangare Na Dakin Bincike Na Farko Na Tashar Sararin Samaniyarta

2022-07-24 16:53:07 CMG Hausa

Yau ne, kasar Sin ta yi nasarar harba na’urar Wentian, wani muhimmin bangare na farko na tashar binciken sararin samaniyarta. Sabon bangaren dakin binciken, zai yi aiki ne a matsayin dandalin gwaji na kimiyya mai karfi.

Mataimakin babban mai tsara tsarin tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin a kwalejin fasahar sararin samaniya ta kasar Sin Liu Gang, ya bayyana cewa, na'urar Wentian tana da tsayin mita 17.9, kana fadinta mafi yawa ya kai mita 4.2, da kuma nauyinta tan 23.

Tsarin Wentian ya kunshi dakin aiki, da dakin adana iska, da kuma dakin adana kayan aiki.

Da misalin karfe 2 da mintuna 22 na rana agogon wurin ne, rokar dakon kaya ta Long March-5B Y3, dauke da na’urar Wentian ne, ta tashi daga wurin harba kumbon sararin samaniyar Wenchang da ke gabar teku a lardin Hainan zuwa sararin samaniya kamar yadda ofishin kula da ayyukan binciken sararin samaniya ta kasar Sin (CMSA) ta bayyana.

A cewar hukumar CMSA, kimanin dakika 495 bayan haka, na’urar Wentian ta rabu da rokar kuma ta shiga cikin falaki cikin nasara kamar yadda aka tsara.

Wannan shi ne karo na 24 na harba kumbuna, tun bayan da aka amince da kaddamar da shirin binciken sararin samaniyar kasar.

A bana ne ake saran kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin mai suna Tiangong. Daga nan ne kuma, za ta rikide daga tsari guda daya zuwa tashar binciken sararin samaniya na kasa, mai dauke da sassa guda, wato Tianhe, da na'urorin bincike guda biyu, na Wentian da Mengtian.

A watan Afrilun shekarar 2021 ne dai, aka harba na'urar Tianhe, kana ana shirin harba na'urar Mengtian a watan Oktoba na wannan shekara.(Ibrahim)