logo

HAUSA

Shugaba Xi ya taya kasar Masar murnar cika shekaru 70 da kafuwar ta

2022-07-23 17:00:03 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da sakon taya murnar cika shekaru 70 da kafuwar kasar Masar, ga takwaransa na Masar din Abdel-Fattah al-Sisi.

Cikin sakon wanda ya aike a Asabar din nan, shugaba Xi ya ce Masar ta ci gaba da bin hanyar nasara bayan samun ‘yancin kai, ta kuma samu bunkasuwa, tare da taka muhimmiyar rawa a harkokin da suka shafi kasa da kasa da na shiyyoyi.

Shugaban na Sin, ya ce kasar sa na mayar da hankali matuka ga bunkasa alakar ta da Masar. Ya ce a shirye yake ya yi aiki tare da shugaba Al-Sisi, ta yadda sassan biyu za su marawa juna baya, da ingiza nasarar shawarar nan ta “ziri daya da hanya daya”, tare da yin hadin gwiwa wajen aiwatar da shawarar ciyar da duniya gaba, da kare moriyar kasashe masu tasowa, da kara azama wajen gina al’ummar Sin da Masar mai makomar bai daya a sabon zamani, ta yadda hakan zai amfani kasashen 2, da ma al’ummun su baki daya. (Saminu Alhassan)