logo

HAUSA

Shugabannin JKS da na kasar sun karbi allurar rigakafin COVID-19 wadda aka sarrafa a kasar

2022-07-23 21:48:55 CMG Hausa

Mataimakin shugaban hukumar kiwon lafiya ta kasar Sin Zeng Yixin, ya ce shugabannin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da jagororin kasar sun karbi allurar rigakafin COVID-19 da aka sarrafa a cikin kasar.

Zeng ya bayyana hakan ne a Asabar din nan, yayin taron manema labarai na tsarin hadin gwiwar kandagarki da shawo kan annoba na majalissar gudanarwar kasar Sin, yana mai cewa "Hakan ya nuna amincewar da rigakafin COVID-19 samfurin kasar Sin ya samu”. Kaza lika karin wasu shugabannin kasashen duniya sama da 30, sun karbi rigakafin samfurin na kasar Sin”

Jami’in ya kara da cewa, akwai nau’o’in rigakafin COVID-19 na Sin guda 3, wadanda hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta amince da amfani da su a matakin gaggawa. Kaza lika sama da kasashe 100 sun samu izinin amfani da nau’oin rigakafin, yayin da da yawa daga cikinsu suka amince da rigakafin ta Sin a matsayin wadda ake iya yiwa yara kanana.

A kasar Sin, an yi wa mutane kusan biliyan 1.3 rigakafin COVID-19. Adadin da ya kai kusan kaso 92.1 bisa dari na daukacin jama’ar kasar. Kuma kimanin kaso 89.7 bisa dari na al’ummar kasar sun karbi alluran karo 2, yayin da kaso 71.7 bisa dari suka karbi karin allurar a zagaye na 3.

Bugu da kari, kasar Sin na aiki domin samar da rigakafin COVID-19 samfurin Omicron.   (Saminu Alhassan)