logo

HAUSA

Kasuwar cinikin takardun bashi ta Sin ta zama muhimmin wurin da ake son zuba jari

2022-07-22 15:51:49 CMG HAUSA

 

Yau da misalin karfe 10 na safe, a yayin taron da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar Sin ya shirya, mataimakiyar shugaban hukumar kula da kudaden musayar kasashen waje ta kasar Sin, kana kakakin hukumar Wang Chunying ta gabatar da yadda aka yi amfani da kudaden musayar kasashen waje a farkon rabin shekarar 2022.

Wang Chunying ta yi bayani cewa, kasuwar takardun bashi ta Sin ta riga ta zama muhimmin wurin a kai a kai da ake son zuba jarin takardun bashi daga ketare a cikin fadin duniya. A cikin ’yan shekarun nan, an bude kasuwar takardun bashi ta Sin a hankali, kuma cinikayyar ketare ta zama sauki, an hada takardun bashi na Sin a cikin manyan ma’aunoni uku na duniya, kuma tasirin da kasuwar takardun bashi a cikin kasar ya karu sosai. A cikin wannan hali, zuwa karshen shekarar 2021, sikelin zuba jarin takardun bashi da Sin ta sha ya kai wajen dalar biliyan 820, wanda ya kai daya bisa uku a cikin rabon zuba jarin takardun bashi daga ketare da sabon tattalin arziki ya sha. Daga shekarar 2017 zuwa shekarar 2021, sikelin kudaden zuba jarin takardun bashi daga ketare da Sin ta sha ya kai matsayi na hudu a duniya. (Safiyah Ma)