logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya aikewa takwaransa na Amurka sakon jajen harbuwa da cutar COVID-19

2022-07-22 20:34:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aikewa takwaransa na Amurka Joe Biden da sakon jaje, game da harbuwa da Mr. Biden din ya yi da cutar COVID-19.

Cikin sakon da ya aike a yau Juma’a, Xi ya ce sakamakon jin wannan labari, yana isar da sahihin sakon jaje ga shugaba Biden, yana mai fatan zai murmure cikin sauri. (Saminu)