logo

HAUSA

An musanta yunkurin Amurka na batawa Sin suna

2022-07-22 14:42:17 CMG HAUSA

 

Shugaban hukumar samar da ci gaba ta kasa da kasa ta kasar Sin CIDCA, Luo Zhaohui, ya musanta wasu jawabai da jami’an Amurka suka yi domin bata sunan Sin dangane da manufar taimakawa kasashen waje.

Luo Zhaohui ya bayyana haka ne yayin taron yaki da cin hanci na hadin gwiwar ci gaban duniya da hukumar CIDCA da m’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin suka shirya tare a jiya.

A cewarsa, kasar Sin ta aiwatar da shirin saukaka biyan bashi na kungiyar G20, inda ta sassauta lokacin biyan bashin sama da dala biliyan 1.3, wanda ya dauki kusan kaso 30 na jimilar basussukan da G20 ta tsawaita lokacin biyansu, lamarin da ya sa ta zama wadda ta fi bayar da gudunmawa ga shirin. (Fa’iza Mustapha)