logo

HAUSA

EU ta bukaci kasashe membobin kungiyar su rage yawan amfani da makamashi da kashi 15

2022-07-21 14:59:39 CMG Hausa

Shugabannin kungiyar tarayyar Turai (EU), sun sanar da wani shiri na rage dogaro da iskar gas na kasar Rasha, yayin da ake fuskantar matsala game da samar da iskar gas din.

Hukumar gudanarwar EU ta yi kira ga kasashe mambobin kungiyar, da su rage yawan makamashin da suke amfani da shi da kashi 15 cikin 100, tsakanin watan Agusta zuwa karshen watan Maris.

Rage amfani da makamashin, ba tilas ba ne, amma shawarwarin da aka gabatar, sun baiwa kungiyar ta EU damar tilasta su, a yayin da aka shiga yanayin gaggawa na amfani da makamashi.

Shugabar hukumar gudanarwar kungiyar Ursula von der Leyen, ta bayyana katsewar iskar gas din baki daya da Rasha ke samarwa, a matsayin wani lamari mai yiwuwa.

An fara samun rashin jituwa kan makamashi tsakanin Moscow da Brussels ne, tun bayan barkewar yakin Ukraine a watan Fabrairu. (Ibrahim)