logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga dandalin raya matasan duniya

2022-07-21 15:39:01 CMG HAUSA

 

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, a Alhamis din nan ya aike da wasikar taya murna, ga dandalin raya matasa na kasa da kasa.

A cikin wasikar tasa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, yana fatan dandalin zai zama wata muhimmiyar kafa ga matasan duniya, wajen ba da gudummawarsu ga ci gaban duniya, tare da sa kaimi ga ci gaban matasa a duniya baki daya.

A yau ne, aka bude dandalin raya matasa na duniya a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, mai taken "Samar da ci gaban matasa da samar da makomar bai daya", wanda kungiyar matasan kasar Sin ta shirya. (Amina Xu)