logo

HAUSA

Kasar Sin ta gargadi Amurka ta daina dauka kowa ma irinta ne

2022-07-21 21:14:58 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta musanta furucin jami’in Amurka dake zargin kasar Sin da neman yin katsalandan cikin zaben kasar, inda ta shawarci Amurkar da ta daina dauka kowa ma irinta, ta rika zargin kasar Sin ba tare da wani dalili ba.

Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ne ya bayyana haka, yayin taron manema labarai na yau Alhamis.

Rahotanni sun ruwaito cewa, daraktan hukumar bincike ta Amurka FBI, Christopher Wray, ya yi gargadin cewa, zaben Amurka na fuskantar barazanar kutse daga Sin da Rasha da Iran da sauran wasu kasashe. A cewarsa, kasar Sin na kokarin ganin faduwar Amurka.

Dangane da haka, Wang Wenbin ya ce, kamar yadda tsohon babban jami’in Amurka ya bayyana a kwanakin baya, kitsa juyin mulki da tsoma baki cikin harkokin gida na wasu kasashe, hallaya ce ta Amurka, irin wannan bai taba zama tsarin kasar Sin ba. Sin na nacewa ne ga kaucewa yin katsalandan cikin harkokin gidan kasashe, kuma ba zata yi katsalandan cikin zaben wasu kasashen ba. A don haka, kasar Sin na shawarartar Amurka da kada ta rika dauka kowa irinta ne, ta zargi kasar Sin babu gaira ba dalili, maimakon haka, ta mayar da hankali kan warware matsalolin dake gabanta. (Faeza Mustapha)