logo

HAUSA

Sin ta mayar da martani ga rahoton shekara-shekara na fataucin bil adama na Amurka

2022-07-20 21:28:28 CMG Hausa

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, Amurka na yin watsi da gaskiya a kowace shekara, tana kuma tattara "rahoto" na karya, kan batun fataucin bil adama don yaudarar duniya.

A hakika dai, Amurka ita ce kasa ta farko a duniya wajen safarar mutane.

A ranar 19 ga wata bisa agogon wurin, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar da rahotonta na shekara-shekara game da fataucin bil-Adama, inda ta ci gaba da sanya kasar Sin a jerin kasashe, da yankuna mafi muni na uku, tare da kai hari, tare da bata sunan kasar Sin kan wasu batutuwa, ciki har da "aikin tilas" a jihar Xinjiang.

Game da haka, kakakin ya nuna cewa, ko ta yaya Amurka ta boye, ba za ta iya wanke laifinta na tarihin zama "kasar cinikayyar bayi" ba, kuma ko ta yaya Amurka ta ba da hujja, ba za ta iya canza halinta na "kasar asali, inda ake wucewa, da yin aikin tilas ba".

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta kiyasta cewa, ana safarar mutane kimanin 100,000 daga kasashen waje zuwa Amurka a kowace shekara domin yin aikin tilas. Bugu da kari, jihohin Amurka 50 da yankin Washington D.C., sun ba da rahoton shari'ar aikin tilas, da fataucin mutane a cikin shekaru biyar da suka gabata.  (Mai fassara: Bilkisu Xin)