logo

HAUSA

An zabi Ranil Wickremesinghe a matsayin shugaban kasar Sri Lanka

2022-07-20 20:10:27 CMG Hausa

‘Yan majalissar dokokin Sri Lanka, sun zabi shugaban rikon kwaryar kasar Ranil Wickremesinghe, a matsayin sabon shugaban kasar a yau Laraba.

Jim kadan bayan zabensa, Wickremesinghe ya yi wa ‘yan majalisar dokokin jawabi, yana mai kira ga magoya bayan sa, da ma ‘yan adawa da su dunkule wuri guda, su yi aiki tare shi, domin baiwa Sri Lanka jagoranci da zai tsame ta daga komadar tattalin arziki da ta fada.

Tsohon shugaban kasar Gotabaya Rajapaksa, ya ajiye mukamin sa ne a makon da ya gabata, biyo bayan zanga zangar da ‘yan kasar suka shiga, domin nuna bacin ran su ga halin matsin tattalin arziki da kasar ta tsunduma.

Bayan ajiye aikin shugaba Rajapaksa, kakakin majalissar dokokin kasar Mahinda Yapa Abeywardena, ya sanar da firaminista Wickremesinghe, a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, kafin kuma a yanzu a zabe shi shugaban kasa. (Saminu Alhassan)