logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Saliyo sun zanta game da alakar kasashen su

2022-07-20 20:22:20 CMG Hausa

Dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya zanta tare da takwaransa na kasar Saliyo David John Francis ta wayar tarho. Yayin zantawar ta ranar Talata, jami’an biyu sun tattauna game da alakar kasashen su.

Mr. Francis, wanda ya fayyace matsayar kasarsa, ya jinjinawa gwamnatin kasar Sin, da al’ummar Sinawa, bisa tallafi mai daraja da suke baiwa Saliyo, a fannin tattalin arziki, da raya zamantakewar al’umma cikin tsawon shekaru. Jami’in ya ce tun barkewar annobar COVID-19, Sin ta gaggauta tallafawa Saliyo, da sauran kasashe kanana da matsakaita, da kayayyakin da ake bukata domin yaki da annobar.

Mr. Francis ya bayyana Sin a matsayin kawar da Saliyo ke iya dogaro da ita, don haka kasar sa za ta ci gaba da mara baya ga kasar Sin, a dukkanin al’amura dake da nasaba da moriyar ta, da sauran muhimman batutuwa, kuma Saliyo za ta zurfafa hadin gwiwa da Sin, a sassa daban daban, kana Saliyo na maraba da karin kamfanonin Sin da ke son zuba jari a yankunan ta.

A nasa bangare, Wang Yi ya ce Sin ta gamsu, da yadda a ko da yaushe Saliyo ke mara baya ga dukkanin moriyar kasar Sin, kuma a nata bangaren, kasarsa ke taimakawa Saliyo a fannin kare ikon mulkin kai da ‘yanci, da martabar kasar.

Wang ya kara da cewa, Sin za ta ci gaba da taimakawa Saliyo gwargwadon bukatar kasar, za ta ingiza hadin gwiwa a fannin hakar ma’adanai, da raya harkar noma da ababen more rayuwa, za ta aiwatar da matakan inganta rayuwar jama’a, da karfafa gwiwar kamfanonin Sin, wajen zuba jarin su a Saliyo, da taimakawa kasar a fannin inganta ikon ta na samar da ci gaba, da gaggauta zamanantar da masana’antunta. (Saminu Alhassan)