logo

HAUSA

Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban dandalin WEF

2022-07-20 10:47:25 CMG HAUSA

 

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya tattauna ta kafar bidiyo da shugaban dandalin tattauna tattalin arzikin duniya, Klaus Schwab.

Li Keqiang, ya ce dangantakar Sin da dandalin WEF ta shafe sama da shekaru 40, kusan lokaci guda da fara aiwatar da manufar kasar Sin ta gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje.

Ya kara da cewa, Sin na yabawa yadda dandalin ke ci gaba da mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziki da hadin gwiwarsa da Sin, kuma zurfin dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, zai taimaka wajen aikewa da kyakkyawan sakon habaka tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a ga duniya.

Firaministan ya ce, Sin za ta nace ga manufarta ta bude kofa tare da hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki wajen inganta tattaunawa da tuntubar juna, domin samar da yanayi mai kyau na hadin gwiwar moriyar juna .

Da yake bayyana dandalin WEF a matsayin wanda ya rike abotarsa da Sin cikin sama da shekaru 40, Klaus Schwab ya ce a shirye dandalin yake ya zurfafa hadin gwiwarsa da Sin, domin inganta tattaunawa a duniya da amfani da rawar da ’yan kasuwa ke takawa da inganta musaya tsakanin kasa da kasa da hadin gwiwa, tare da taka muhimmiyar rawa wajen tunkarar kalubalen yanayi da ingiza sauye-sauye a ayyukan masana’antu da kuma tabbatar da adalci a tsakanin al’umma. (Fa’iza Mustapha)