logo

HAUSA

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar rikicin kabilanci a Sudan ya karu zuwa 105

2022-07-20 10:46:45 CMG HAUSA

 

Hukumomin lafiya a Sudan, sun ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar rikicin kabilanci a jihar Blue Nile dake kudu maso gabashin kasar, ya karu zuwa 105. 

Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta jihar Blue Nile ta fitar a jiya Talata, ta ruwaito Omer Adam Omer, shugaban sashen kula da daukin gaggawa da tunkarar annoba na ma’aikatar na cewa, tun bayan barkewar rikicin, mutane 105 sun mutu, wasu 225 kuma sun ji rauni, yayin da 8,470 suka rasa matsugunansu.

Ya ce mutane 20 daga cikin wadanda suka ji rauni, na cikin yanayi mai tsanani, inda aka turasu Khartoum, babban birnin kasar, domin jinya.

Rikicin ya barke ne tsakanin kabilun Hausa da Berta a yankuna da dama na jihar Blue Nile, biyo bayan kisan wani manomi da aka yi a yankin Gisan na jihar.

Rikicin ya bazu zuwa wasu yankunan jihar, inda gomman mutane suka mutu ko suka jikkata, tare da tilastawa dubbai tserewa daga gidajensu. (Fa’iza Mustapha)