logo

HAUSA

Sin ta gargadi Amurka game da abun da zai biyo bayan ziyarar Nancy Pelosi a yankin Taiwan

2022-07-19 20:51:50 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce gwamnatin kasar Sin na jan kunnen Amurka, da ta dakatar da shirin da kakakin majalissar wakilanta Nancy Pelosi ke yi, na ziyartar yankin Taiwan na kasar Sin. Kuma idan har Pelosi ta gudanar da wannan ziyara, kasar Sin za ta mayar da martani mai karfi, kuma Amurka ce za ta dauki alhakin duk abun da ya biyo baya.

Zhao ya bayyana hakan ne, yayin taron manema labarai na Talatar nan, yana mai cewa, bangaren Sin ya sha nanata rashin amincewa, da duk wani nau’in ziyara da jami’an Amurka za su kai yankin na Taiwan, kuma yin hakan zai sanya Sin aiwatar da matakai masu karfi, na kare ikon ta na mulkin kai, da tsaron yankunan ta.

Ya ce majalissar dokokin bangare ne na gwamnatin Amurka, don haka duk wani jami’in majalissar ya wajaba, ya martaba manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Jaridar Financial Times ta rawaito cewa, Pelosi na shirin ziyartar yankin Taiwan cikin watan Agusta mai zuwa, ko da yake jaridar ta ce akwai rabuwar kawuna tsakanin jami’an gwamnatin Amurka, game da yiwuwar gudanar da ziyarar.

Kafin hakan, mahukuntan Sin sun nuna matukar rashin amincewa, tare da gabatar da korafi ga bangaren Amurka, don gane da ziyarar da Pelosi ta shirya kaiwa yankin na Taiwan a watan Afirilun da ya shude, inda daga bisani jami’ar ta ce ta dage ziyarar, saboda harbuwa da ta yi da cutar COVID-19.  (Saminu Alhassan)