logo

HAUSA

AfDB ya amince da dala miliyan 11 ga sakatariyar AfCFTA don bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka

2022-07-19 10:01:25 CMG Hausa

Bankin raya Afirka (AfDB), ya amince da ba da tallafin dalar Amurka miliyan 11 ga sakatariyar yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka (AfCFTA) don bunkasa ayyukan cinikayya cikin 'yanci na nahiyar.

Sanarwar da bankin ya fitar jiya Litinin ta ce, tallafin na baya-bayan nan, shi ne karo na biyu da aka baiwa sakatariyar ta AfCFTA, bayan dala miliyan biyar da bankin ya bayar, bayan bude sakatariyar a Accra, babban birnin Ghana a watan Agustan shekarar 2020.

Sanarwar ta ce, tallafin na biyu zai kuma ciyar da ajandar hadakar kasuwanci ta Afirka gaba, ta hanyar baiwa sakatariyar da kasashe mambobinta damar yin hakan.

Darektan sashen bunkasa masana’antu da kasuwanci na bankin, Abdu Mukhtar ya bayyana cewa, amincewar hukumar darektocin bankin ta bayar da tallafin, zai baiwa sakatariyar AfCFTA damar tabbatar da daidaito, da hangen nesa, da yin ciniki cikin ’yanci a nahiyar. (Ibrahim)