logo

HAUSA

Wang Yi ya tattauna da mashawarcin shugaban Faransa kan harkokin waje ta wayar tarho

2022-07-19 14:01:58 CMG Hausa

Dan majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, jiya Litinin ya tattauna ta wayar tarho da mai baiwa shugaban kasar Faransa shawara kan harkokin waje Emmanuel Bonne.

Wang Yi ya bayyana cewa, bayan sake zabar shugaba Emmanuel Macron, shugabannin kasashen biyu sun samu nasarar ganawa, wanda ya samar da jagoranci don samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ga ci gaban alakar kasashen biyu da kuma samar da sabon kuzari.

Bangarorin biyu sun gaggauta aiwatar da muhimman ra’ayoyin da shugabannin kasashen suka cimma, kuma dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta fara aiki yadda ya kamata. Bangaren kasar Sin yana son yin aiki tare da bangaren Faransa, don inganta bunkasuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Faransa.

A nasa jawabin Bonne ya bayyana cewa, bangaren Faransa yana dora muhimmanci sosai kan ci gaba da yin mu'ammala mai inganci tsakanin kasashen biyu, kuma shugaba Macron ya tsaya tsayin daka kan sada zumunta tare da Sin, da fatan ci gaba da inganta dangantakar abokantaka tsakanin Faransa da Sin zuwa wani sabon matsayi. Bangaren Faransa yana fatan zurfafa hadin gwiwa tare da Sin a fannonin sufurin jiragen sama, da amfanin gona da kayayyakin abinci, da makamashi da al’adu da dai sauransu, da karfafa yin mu’ammala a harkokin duniya kamar kare nau’o’in halittu da tinkarar sauyin yanayi. Yana kuma fatan bangarorin biyu, za su gudanar da wani sabon zagayen tattaunawa cikin sauri. (Safiyah Ma)