logo

HAUSA

Sakataren MDD ya yi kira da a dauki tsauraran matakai kan matsalar abinci a duniya

2022-07-19 11:10:39 CMG Hausa

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira da a dauki managartan matakai a kuma zahiri don magance matsalar karancin abinci da ake fama da ita a duniya.

Guterres wanda ya yi wannan gargadi jiya Litinin a jawabin da ya gabatar ta kafar bidiyo ga babban taron MDD na musamman mai taken "Lokaci na yin aiki tare: Tsara manufofin magance matsalar abinci da duniya ke fama da ita”. Ya bayyana cewa, muna fuskantar hadarin gaske na yunwa mai tarin yawa a wannan shekara. Kuma shekara mai zuwa na iya zama mafi muni."

Jami’in na MDD ya kuma bayyana cewa, “za mu iya kaucewa wannan bala'i, idan muka dauki mataki yanzu”, “muka kuma yi aiki tare, don tsara managartan manufofi da matakai a zahiri.”

Hakan a cewarsa, yana nufin dawo da Ukraine cikin tsarin samar da abinci nan take, da abinci da takin da Rasha ke samarwa, zuwa kasuwannin duniya, da kuma bude kasuwancin duniya.

Guterres ya kuma jaddada bukatar tinkarar matsalar kudi a kasashe masu tasowa, da gaggauta bude duk wata hanyar da za a iya amfani da ita, don bunkasa kariyar zamantakewa, da tallafawa kananan manoma da iyalai, don kara yawan amfanin gonan da suke samarwa, da kuma dogaro da kai.

Ya kara da cewa, duk wadannan suna nufin canza tsare-tsaren samar da abinci a kowane mataki, don sanya abincin ya zama mai araha, da lafiya da dorewa a tsakanin kowane mutum, a ko'ina a duniya. (Ibrahim)