logo

HAUSA

Rokar harba kumbon Wentian ta isa tashar Wenchang dake lardin Hainan

2022-07-18 21:11:52 CMG Hausa

Rokar harba kumbuna ta “Long March-5B Y3”, wadda za a yi amfani da ita wajen harba kumbon dakin binciken sararin samaniya na Wentian, ta isa tashar harba kumbuna ta Wenchang, dake lardin Hainan na kudancin kasar Sin.

Rahotanni sun ce rokar ta isa tashar ne da sanyin safiyar Litinin din nan. Kuma nan da ‘yan kwanaki masu zuwa, za a gudanar da ayyukan gwaje gwaje, na tabbatar da nagartar harba kumbo da za a yi da rokar.  (Saminu)