logo

HAUSA

Jami’an tsaron Afghanistan sun harbe mayakan IS guda uku

2022-07-18 13:47:54 CMG Hausa

Wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake Kabul ya labarto a jiya cewa, kakakin gwamnati mai wucin gadi ta Afghanistan Zabihullah Mujahid ya bayyana a kafofin sada zumunta cewa, jami’an tsaro sun kaddamar da wani samamen fatattakar ’yan ta’addar daular musulunci wato IS a lardin Kunduz dake arewacin kasar a daren ranar 16, inda suka yi nasarar kashe 'yan bindiga guda uku kuma kama wasu guda 5.

A cikin watanni biyu da suka gabata, an sha samun labarun kai hare-hare a fadin kasar Afghanistan, lamarin da ya haifar da hasarar rayuka da dama. Kungiyar IS ta yi ikirarin kai hare-hare da dama kan makarantu da masallatai da motocin bas-bas. (Safiyah Ma)