Iran: Amurka tana amfani da manufar tsoron Iran don tada rikici a yankin gabas ta tsakiya
2022-07-18 11:16:14 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Nasser Kanaani, ya bayyana a jiya cewa, kasar Amurka tana ci gaba da amfani da manufar tsoron Iran, da ba ta yi nasara ba, do neman tada zaune tsaye a yankin gabas ta tsakiya.
A sanarwar da aka fitar a wannan rana, Kanaani ya musanta kalaman da shugaban kasar Amurka Joseph Biden, ya yi na kyamar kasar Iran yayin da yake ziyara a yankin gabas ta tsakiya. Sanarwar ta ce, wannan ita ce manufar da gwamnatin kasar Amurka ta kan yi amfani da ita, don tada rikici a wannan yanki.
Kanaani ya ce, kasar Amurka tana tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashen dake yankin, da kaddamar da mamayar soja da wuce gona da iri, da sayar da tarin makamai da sanar da kara karfin soja a yankin. Ya kara da cewa, kasar Iran tana fatan gwamnatocin kasashen yankin gabas ta tsakiya, za su amsa kiran kasar Iran na yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakaninsu, su dauki matakai masu dacewa don tabbatar da tsaro da zaman lafiya da samun bunkasuwa tare a yankin.
Ziyarar da Biden ya kai Isra'ila, da gabar yammacin kogin Jordan da Saudiyya daga ranar 13 zuwa 16, ita ce ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta tsakiya tun bayan hawansa mulki. A yayin da yake halartar taron koli na kiyaye tsaro da samun bunkasuwa a kasar Saudiyya a ranar 16 ga wata, Biden ya bayyana cewa, aikin Iran yana kawo illa ga zaman lafiyar yankin, kuma kasar Amurka ba za ta taba bari Iran ta mallaki makaman nukiliya ba. (Zainab)