logo

HAUSA

Rahoton Amurka ya ci gaba da shara karya da yada jita-jita kan batutuwan da suka shafi Xinjiang

2022-07-18 20:00:50 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka, ta gabatar da rahoto ga Majalisar Dokokin kasar a ranar 14 ga wata, kuma ta fitar da "Dabarun Hasashe, Hanawa, da Amsa Ayyukan Ta'addanci" na farko a tarihin kasar.

Abubuwan da ke da alaka da kasar Sin a cikin rahoton, sun sake zargin kasar Sin da aikata abun da aka kira "kisan kare dangi", da "laifuffukan cin zarafin bil'adama" a jihar Xinjiang ta kasar, har da ma abun da aka kira da "aikin tilas" a jihar.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya nuna cewa, a wasu lokuta da suka gabata, bisa kitsa karya, Amurka ta shirya, tare da ci gaba da yada abun da aka kira "kisan kare dangi", da "aikin tilas" da "laifi kan bil'adama" da sauran karairayi, don bata suna, da saka takunkumi da murkushe kasar ta Sin.

Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin za ta dauki dukkan matakan da suka dace don kare muradu, da tsaro da kuma ci gabanta. Ko shakka babu yunkurin da Amurka ta yi na yada karairayi da ke da alaka da jihar Xinjiang, da yin amfani da batutuwan da suka shafi Xinjiang wajen tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin zai bi ruwa. (Mai fassara: Bilkisu Xin)