logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Hungary sun yi shawarwari kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma batun Ukraine

2022-07-18 11:20:18 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwaransa na kasar Hungary Peter Szijjarto, sun tattauna ta wayar tarho jiya Lahadi, kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma rikicin Ukraine.

A yayin tattaunawar da bangaren Hungary ya shirya, Szijjarto ya yi wa Wang Yi karin haske game da halin da ake ciki a kasashen Turai da Hungary, musamman kalubalen tattalin arziki da na kudi da kasar Hungary ke fuskanta, sakamakon tasirin rikicin Ukraine.

Wang ya ce, kasar Sin ba ta da hannu cikin wannan batu, ba ta tsoma hannu a ciki ba, kuma ba za ta kara ruruta wutar rikicin ba. Ya kara da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da karfafa yin shawarwari da tattaunawar zaman lafiya.

Wang ya ce, ya yi imanin cewa, kasar Hungary za ta ci gaba da tsayawa kan matsayi na gaskiya da sanin ya kamata, da kuma matsawa kungiyar tarayyar Turai lamba, ta hanyar daukar matakan da suka dace kan kasar Sin.

A nasa jawabin, Szijjarto ya ce, kasar Sin ba ta taba zama abokiyar adawar Turai ba, sai dai abokiyar huldar dake kawo damammaki na hadin gwiwa.

Ya kara da cewa, bangaren Hungary zai ci gaba da kara kaimi wajen inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen Turai da Sin da ke mutunta juna, da daidaito da kuma moriyar juna. (Ibrahim Yaya)