logo

HAUSA

Jirgin saman Ukraine dauke da harsasai ya fadi a kasar Girka

2022-07-17 20:58:54 CMG Hausa

Jirgin saman dakon kaya mallakar Ukraine, dauke da harsasai da ya taso daga Serbia zuwa Bangladesh, ya fadi a kusa da birnin Kavala na kasar Girka, inda dukkanin ma’aikatan jirgin 8 suka mutu. Haka kuma wasu kayayyaki masu hadari, sun watsu a wurin da jirgin ya fadi.

Hotunan da karamin jiragin daukar hoto ya dauka, sun nuna tarkacen jirgin Antonov An-12 na konewa a wurin. Hukumomin kasar Girka sun ce mutane 8 ne a cikin jirgin, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen Ukraine, ya ce dukkansu, ‘yan asalin kasar ta Ukaine ne.