logo

HAUSA

Kasar Sin za ta inganta manufofin taimakawa dukkan bangarorin tattalin arziki

2022-07-17 17:31:30 CMG Hausa

Biyo bayan koma bayan da aka fuskanta sanadiyyar annobar COVID-19 da sauran matsaloli daga waje, babban bankin kasar Sin, zai inganta aiwatar da wasu manufofin kudi domin taimakawa dukkan bangarorin tattalin arziki.

Yayin taro karo na 3 na ministocin kudi na kasashen G20 masu karfin tattalin arziki, Gwamnan babban bankin kasar Sin Yi Gang, ya gabatar da sabon bayani game da ci gaban tattalin arziki da harkokin kudi na Sin yayin taron, yana mai cewa hauhawar farashin kayayyaki na matsakaicin mataki, kuma ana sa ran matakin zai daidaita.

Ya ce bankin zai inganta samar da tsarin taimakawa manyan kamfanoni rage fitar da hayaki mai guba da inganta hadin gwiwar aiwatar da matakan tunkarar sauyin yanayi na G20, ta yadda bangaren hada-hadar kudi zai samu damar taimakawa manufofin kai wa matsayin koli na fitar da hayaki mai guba da kuma cimma daidaito tsakanin hayakin da abubuwan dake shawo kansa.

Taron, karkashin shugabancin Indonesia, ya gudana ne a birnin Bali, a ranekun 15 da 16 ga wata inda aka samu mahalarta a zahiri da kuma ta kafar bidiyo. Yayin taron, an kuma tattauna game da tattalin arzikin duniya da ajandar kiwon lafiya ta duniya da tsarin hada-hadar kudi na kasa da kasa da da zuba jari kan ababen more rayuwa da kuma batun haraji na duniya.