logo

HAUSA

Karuwar kudin shigar manyan kamfanonin Sin a rabin farkon bana ta zarce hasashen da aka yi

2022-07-16 15:58:48 CMG Hausa

Rahotannin hukumar kula da kadarorin kasa ta majalisar gudanarwar kasar Sin sun nuna cewa, karuwar kudin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiyar kasar a rabin farko na bana, ta zarce hasashen da aka yi, kuma ingancin ci gabansu yana kara kyautatuwa.

Jimillar adadin kudin shigar manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, ta kai yuan triliyan 19.2, adadin da ya karu da kaso 12 bisa dari a kan makamancin lokacin a bara. Kuma jimillar ribarsu, ta kai yuan biliyan 1409.36, adadin da ya karu da kaso 7.1. Kana adadin ribar da suka samu bayan da suka biya haraji, ya kai yuan biliyan 1085.75, adadin da ya karu da kaso 6.1 bisa dari.

An samu wannan ci gaba ne biyo bayan manufofi goma na sa kaimi kan ci gaban manyan kamfanonin kasar da hukumar kula da kadarorin kasar ta fitar.

Hakazalika, manyan kamfanoni mallakar gwamnatin tsakiya ta kasar Sin, sun ba da babbar gudummowa wajen zuba jari, inda sauran kamfanonin sana’o’i daban daban na kasar suka ci gajiya. Ana iya cewa, sun taimakawa bunkasar tattalin arzikin kasar Sin matuka cikin watanni shida na farkon bana. (Jamila)