logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a kyautata dokoki domin samun ci gaba mai dorewa a bangaren teku

2022-07-16 15:28:06 CMG Hausa

Zaunannen wakilin Sin a MDD Zhang Jun, ya yi kira da a karfafa kiyaye dokoki a bangaren harkokin teku domin bunkasa samun ci gaba mai dorewa.

A cewarsa, tekuna na kyautata rayuwa, kuma suna dauke da albarkatu. Sannan, sun kasance mahadar sassan duniya, tare da samar da dandali mai muhimmanci na inganta ci gaba mai dorewa. Ya ce a yanzu, tsarin tafiyar da harkokin teku a duniya na fuskantar kalubale, kamar gurbatar muhalli da sauyin yanayi, da karuwar matakin teku. Kuma, kasa daya tilo ba za ta iya magance wadan nan matsaloli ba, har sai kasa da kasa sun hada hannu wajen daukar mataki.

A cewarsa, ya kamata a hada hannu wajen inganta huldar kasa da kasa da kare tsarin huldar karkashin dokokin MDD, da kiyaye odar ruwan bisa dokokin kasa da kasa, da yayata aiwatar da ajandar ci gaba mai dorewa da ake son cimmawa zuwa 2030.

Haka kuma, ya ce a shirye Sin take ta hada hannu da dukkan bangarori wajen kiyaye dokokin kasa da kasa da suka shafi harkokin teku da tabbatar da tsaro da zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)