logo

HAUSA

Sin ta mika kaso na 2 na tallafin kayan abinci ga Sri Lanka

2022-07-15 19:51:53 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce Sin ta yi nasarar mika kaso na 2 na kayan abinci, na tallafin gaggawa ga kasar Sri Lanka, wadda ke fama da matsanancin yanayin siyasa.

Wang Wenbin, wanda ya bayyana hakan yayin taron manema labarai na Juma’ar nan, ya ce an mika tallafin ne a jiya Alhamis. Ya ce a matsayin ta na kawa, kuma makwafciya ga Sri Lanka, har kullum, kasar Sin na mayar da hankali ga halin matsi, da kalubale da Sri Lanka ke fuskanta a yanzu, tana kuma ci gaba da samar da taimako gare ta, a fannonin tattalin arziki da ci gaban zamantakewar al’umma iya karfin ta.

Tuni kasar Sin ta sanar da aniyar ta, ta tallafawa Sri Lanka da agajin jin kai na kudin Sin yuan miliyan 500. (Saminu)