logo

HAUSA

Xi ya yi rangadin aiki a jihar Xinjiang

2022-07-15 10:00:21 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin koli na JKS Xi Jinping ya ziyarci jami'ar Xinjiang, da yankin tashar ruwa ta kasa da kasa ta Urumqi, da al'ummar Guyuanxiang dake gundumar Tianshan, da gidan adana kayan tarihi na jihar Xinjiang ta kabilar Uygur mai cin gashin kanta dake birnin Urumqi, babban birnin jihar Xinjiang dake yankin arewa maso yammacin kasar Sin, daga yammacin ranar Talata zuwa safiyar ranar Laraba.

Xi ya fahimci yadda ake aikin zakulo masu hazaka, da yadda ake daidaita matakan yaki da annobar COVID-19 da ci gaban tattalin arziki da zamantakewa tare, da inganta hadin kan kabilu da bunkasuwa, da karfafa fahimtar al'ummar kasar Sin, da dai sauransu.(Ibrahim Yaya)