logo

HAUSA

Cinikin wajen Sin ya karu da kashi 9.4% a watanni 6 na farkon bana

2022-07-15 10:52:02 CMG HAUSA



Alkaluman da babbar hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a kwanakin baya sun nuna cewa, daga watan Jarairu zuwa watan Yuni na bana, kayayyakin da kasar Sin ta shigi da fici, sun karu da kashi 9.4% kan makamancin lokacin bara.

Kakakin ma’aikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting ta shedawa manema labarai jiya Alhamis cewa, a cikin watanni shida na farkon bana, cinikayyar waje ta Sin, ta magance matsaloli da dama da suka kunno kai cikin gida da kuma waje, tare da nuna karfin bunkasuwa ba tare da tangarda ba. Ta ce:

“Yawan kudin dake shafar cinikin shige da fice a watan Yuni, ya kai sabon matsayi a kowane wata. Yadda ake fitar da kayayyaki daga yankin Delta na mashigin kogin Yangtze yana farfadowa cikin sauri, wanda ya karu da kashi 9.3% a farkon watanni 6 na bana. Matakin da ya tabbatar da kasar Sin ta zauna a kan matsayin kasa mafi girma wajen cinikin kayayyaki a duniya. Sannan yawan kudin dake shafar fitar da kayayyaki a watan Jarairu zuwa Maris a kasuwar duniya, ya kai kashi 14.1%, daidai da na makamancin shekarar bara.”

Shu Jueting ta ce, a sauran watanni shida na wannan shekara, yayin da ake ci gaba da fuskantar wasu dalilai na rashin tabbas, da rashin kwanciyar hankali a kasuwannin gida da na waje, ma’aikatar za ta mayar da hankali wajen tabbatar da samun bunkasuwa mai inganci ba tare da tangarda ba ga kamfanonin waje da tsarin samarwa da rarraba kayayyaki a wannan fanni, da taimakawa kamfanoni da habaka kasuwanni da bullo da sabbin hanyoyin samun bunkasuwa da sauransu. (Amina Xu)